logo

HAUSA

Hadiya Abdulla ‘yar Tanzaniya: Kashgar Shi ne Garina

2024-05-20 16:10:27 CMG Hausa


Yankin Kashgar dake jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta, yana can cikin yammacin kasar Sin kusa da kan iyaka da kasashen Kyrgyzstan, Tajikistan, Afghanistan da Pakistan. A zamanin da, Kashgar ya kasance muhimmiyar cibiyar kasuwanci a kan hanyar siliki. An sake farfado da shi tun lokacin da aka samar da shirin shawarar “Ziri daya da hanya daya” ko BRI a shekarar 2013. Yanzu ya zama cibiyar kasuwanci mai cike da kai-komo.

Dilshat Tursun da matarsa Hadiya Msham Abdulla daga kasar Tanzaniya suna gudanar da dakin shan kofi mai suna “Dakin shan kofi na Dili da Diya” a Kashgar. Dakin shan kofi din ya shahara ba wai kawai don dandano da kasancewar kofin na Afirka mai dadi ba, har ma da labarin soyayyar masu shi. Yayin da suke samar da kofi mai kyau, ma'auratan su kan ba kwastomominsu labarin yadda suka hadu kuma suka fara soyayya, duk da kasancewar tazarar dubun dubatar kilomita a tsakaninsu.

Yayin da ake kara zurfafa hadin gwiwa da mu'amala tsakanin Sin da kasashen Afirka, Hadiya Abdulla ta isa kasar Sin a shekarar 2012, inda ta karanci likitanci a jami'ar likitanci ta Fujian dake Fuzhou, hedkwatar lardin Fujian dake kudu maso gabashin kasar Sin.

A shekara ta 2013, Dilshat Tursun ya bar garinsa Yecheng dake yankin Kashgar, don ya karanci ilimin gudanarwa a Jami'ar Fuzhou, shi ma a birnin Fuzhou. A lokacin, bai taba tunanin zai gamu da soyayyar rayuwarsa a cikin shekaru uku ba.

Dilshat Tursun ya sa Hadiya Abdulla a idonsa a lokacin da ake gudanar da wani aiki tsakanin jami’o’i daban daban. Bayan haka sun hadu a lokuta da dama. Suna da muradu da yawa masu kamanceceniya, kuma sun kulla abota. Sau da yawa su kan hadu don yin karatu, wasu lokutan kuma don cin abinci.

"Tanzaniya kasa ce ta Afirka da shawarar ‘ziri daya da hanya daya’ ta BRI ta shafa. Shi ma Kashgar yanki ne mai mahimmanci da shawarar ta shafa. A lokacin, muna yawan cewa shawarar BRI ce ta hada mu," a cewar Dilshat Tursun.

A shekarar 2018, Hadiya Abdulla ta koma garinsu, domin kammala horon sanin makamar aiki na shekara daya, daga bisani kuma ta zama likita mai lasisi, yayin da Dilshat Tursun ya yi aiki a Fuzhou. Rabuwarsu ya sa sun kara fahimtar yadda suke kaunar zama tare. Bayan ta kammala horon, Hadiya Abdulla ta shaida wa iyalinta cewa tana son komawa kasar Sin, domin ta auri Dilshat Tursun. A karshe iyalinta sun amince, ba wai don soyayyar ma'auratan kadai ba, har ma saboda garinsu ya amfana da kungiyoyin likitocin kasar Sin da ayyukan more rayuwa da Sinawa suka gina. Irin wadannan abubuwa sun sa iyalinta son yin mu’amala da Sinawa.

Bayan sun shafe shekaru suna soyayya, sun yi aure a ranar 20 ga Mayu, 2020, kalmar dake kama da "Ina son ka/ki" idan an furta shi cikin harshen Sinanci. A shekarar 2022, lokacin tana da ciki, Dilshat Tursun ya kai Abdulla garinsu, domin ya kula da ita.

Abdulla ta bayyana cewa, "Kashgar wuri ne mai kyan gani da ban sha'awa. Ina son shi sosai. Mutane a nan suna da kyau sosai, kuma suna taimaka mana da duk wata matsala da muke da ita. Duk da cewa ina zaune a wata kasa, mutane masu karamci sun kula da ni tamkar a gidana nake. Kashgar garin mijina ne kuma garin dana ne, kuma garina ne."

Ma'auratan sun fara sana'arsu mai nasaba da kofi a Kashgar, tare da yin tsokaci game da karuwar shan kofi na kasar Sin, da kuma tattalin arzikin Kashgar. Dilshat Tursun ya ce, “Tun da aka ba da shawarar BRI, tsohon birnin Kashgar ya sake samun daukaka a matsayin hanyar bude kofa ga kasashen ketera. Kashgar ya samu bunkasuwa cikin sauri cikin shekarun da suka gabata. Akwai babbar dama ga fara kasuwanci.” 

A watan Maris na 2023 ne ma'auratan suka bude dakin shan kofi na Dili da Diya, a wani wurin shan iska dake cikin tsohon garin Kashgar. Sun saka zuciyarsu da ransu a cikin sana’ar, musamman wajen samar da kofi na Afirka mai dadi. Kashgar yana da dogon tarihin al'adun shayi. Dilshat Tursun ya kware wajen hada shayi tun yana karami. Har ila yau, dakin shan kofi din yana samar da shayi mai kamshi da shayin ‘ya’yan itatuwa.

Dilshat Tursun ya bayyana cewa, "muna hada latte dinmu da madarar gida da kuma waken kofi na Afirka, kamar dai Kashgar, wuri mai kunshe da al'adu daga Gabas da Yamma. Bugu da kari kuma, dakin shan kofi dinmu yana samar da kofi na Afirka da kuma shayi na Sinawa, kamar yadda dangantakar al'adu ta kasance tsakanin Sin da Tanzaniya."

Godiya ga shawarar BRI, waken kofi na Afirka ya samu kason kasuwa mai yawa a kasar Sin a cikin 'yan shekarun nan. Waken kofi na Tanzaniya, wadanda ma'auratan suka shigo da su zuwa Kashgar, sun samu karbuwa, wanda ya zarce tsammaninsu. Suna shirin shigo da karin waken masu inganci daga Tanzaniya, da kuma wasu kasashen Afirka, zuwa Kashgar da sauran yankunan kasar Sin. "Ana daukar lokaci mai tsawo kafin a yi jigilar wake daga Afirka zuwa kasar Sin, kuma kudin dakon jiragen sama ya yi yawa. Da taimakon shawarar BRI, za mu sa tsarin shigo da kayayyakin ya yi sauki, a farashi mai kyau," in ji Abdulla.

Dakin shan kofi na Dili da Diya ya zama sanannen wuri a cikin Kashgar. Dakin shan kofi din da labarin soyayyar ma'auratan ya ja hankalin matafiya marasa adadi, daga ko ina cikin kasar. Haka kuma ma'auratan suna bayar da labarunsu da hajarsu ga duniya, ta hanyar watsa shirye-shiryen kai tsaye a kafofin sada zumunta.

Abdulla ta ce, "ina fatan za mu iya bude jerin shaguna a kowane birni na Xinjiang, ta yadda masoyanmu za su ji dadin kofi na Afirka a duk inda suke. Muna kuma fatan tallata shahararrun kayayyakin Kashgar ga mutane da yawa a Afirka."(Kande Gao)