logo

HAUSA

Amurka za ta janye dukkan sojojinta daga Nijar kafin ran 15 ga watan Satumba

2024-05-20 11:10:47 CMG Hausa

 

Wakilan hukumomin tsaro na jamhuriyar Nijar da Amurka, sun fitar da hadaddiyar sanawa a birnin Niamey, fadar mulkin jamhuriyar Nijar, bayan tatattaunawar da suka shafe kwanaki suna yi, inda bangarorin biyu suka amince da cewa, sojojin Amurka za su janye daga kasar kafin ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa.

Sanarwar da aka fitar a jiya Lahadi, ta nuna cewa, bangarorin biyu za su tabbatar da ayyukan tsaro yayin da sojin Amurka ke janyewa daga kasar.

Kazalika, sanarwar ta bayyana cewa, janyewar sojin Amurka daga Nijar ba za ta illata huldarsu ta raya kasashen biyu ba, inda za su ci gaba da tuntubar juna a fannin diplomasiyya, tare da dukufa kan hadin gwiwa a bangarorin da suke jawo hankulansu, ta yadda za a wanzar da makomar huldarsu a nan gaba. (Amina Xu)