Xi ya aike da sakon ta’azziya ga mataimakin shugaban Iran na farko kan rasuwar Raisi
2024-05-20 18:48:39 CMG Hausa
Yau Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta’azziya ga mataimakin shugaban Iran na farko Mohammad Mokhber, game da rasuwar shugaban kasar Seyed Ebrahim Raisi a cikin hadarin jirgin sama mai saukar ungulu.
A madadin gwamnati da al’ummar kasar Sin, Xi Jinping ya bayyana bakin ciki da juyayin rasuwar shugaban, kuma ya mika ta’aziyya ga mataimaki na farko na shugaban Iran, Mohammad Mokhber, da iyalan shugaba Raisi, da gwamnatin Iran da al’ummar kasar.
Xi ya bayyana cewa, tun da shugaba Raisi ya kama mulki a Iran, ya ba da muhimmiyar gudummawa wajen kiyaye tsaro da kwanciyar hankali, da inganta ci gaba da wadata a kasar, kuma ya yi kokari matuka domin ingantawa da zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakanin Sin da Iran. Ya kuma bayyana rasuwar shugaba Raisi a matsayin babbar hasara ga al’ummar Iran, yana mai cewa al’ummar Sinawa su ma sun rasa wani aboki na gari.(Safiyah Ma)