Iran tana iyakacin kokarin lalubo jirgin sama mai saukar ungulu da ya yi hadari dauke da shugaban kasar
2024-05-20 10:34:15 CMG Hausa
A jiya Lahadi, kafar yada labarai ta kasar Iran ta ba da labarin cewa, wani jirgin sama mai saukar ungulu dauke da shugaban kasar Ebrahim Raisi, da wasu manyan jami’ai ya yi hadari, inda ya yi saukar gaggawa a lardin Azarbaijan ta gabas dake arewa maso yammacin kasar. Kaza lika, kawo yanzu ba a kai ga tabbatar da halin da mutanen dake cikin jirgin ke ciki ba tukuna, sai dai ana ta kokarin aiwatar da aikin ceton.
Gidan talibijin na kasar Iran, ya labarta cewa, mai yiwuwa hadarin ya auku ne a gundumar Varzaqan dake da nisan kilomita 670 daga birnin Tehran fadar mulkin kasar, ko da yake kawo yanzu ba a san inda jirgin yake ba.
An jiyo wakilin gidan talabijin din dake wurin na cewa, aikin ceto na yin tafiyar hawainiya sakamakon yanayin sanyi, da hazo a yankin da ake tsammanin bacewar jirgin. (Amina Xu)