logo

HAUSA

Wang Yi: A tsaya kan manufar kasancewar kasar Sin daya tak don tabbatar da zaman lafiya a yankin mashigin teku na Taiwan

2024-05-20 19:21:15 CMG Hausa

A yau Litinin, ministan harkokin wajen kasar Sin, kana mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, Wang Yi, ya yi furuci dangane da "bikin rantsuwar kama aiki" da "shugaba" na wai  yankin Taiwan ya yi a yau din, yayin da yake halartar taron ministocin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) a birnin Astana na kasar Khazakstan. Jami'in na kasar Sin ya jaddada muhimmancin tsayawa kan manufar kasar Sin daya tak a duniya, don tabbatar da zaman lafiya a yankin mashigin teku na Taiwan.

A cewar Mista Wang, kada a keta babbar manufar kasancewar kasar Sin daya tilo a duniya, saboda manufar ta nuna gaskiyar tarihi, da ma'anar dokokin kasa da kasa.

Ban da haka, jami'in na kasar Sin ya ce yunkurin balle yankin Taiwan daga kasar Sin, ta hanyar wai "'yantar da" yankin Taiwan, ba zai taba samun nasara ba. Kana tabbas za a samu dinkewar sassan kasar Sin waje guda a nan gaba. 

Sa'an nan, yayin da Wang Yi yake ganawa da manema labaru a birnin na Astana, ya bayyana juyayin rasuwar shugaban kasar Iran, da ministan harkokin wajen kasar, sakamakon hadarin jirgin sama. (Bello Wang)