An kaddamar da bikin nuna kayayyakin fasahohin al'adu masu alaka da gasar Olympics a Shanghai na Sin
2024-05-19 21:11:44 CMG Hausa
A yau Lahadi, an kaddamar da bikin baje kolin kayayyakin fasahohin al'adu masu alaka da gasar wasannin Olympics, a birnin Shanghai na kasar Sin. Thomas Bach, shugaban kwamitin shirya gasar Olympics na kasa da kasa, da Shen Haixiong, shugaban babban gidan rediyo da telabijin na Sin (CMG), sun halarci bikin kaddamar da bikin baje kolin mai taken "Daga Beijing zuwa Paris, ziyarar kwararru masu fasahohin al'adu na kasar Sin da ta shafi wasannin Olympics", wanda CMG ke daukar nauyin gudanar da shi. (Bello Wang)