logo

HAUSA

An kammala aikin gina cibiyar nazarin alluran rigakafin cututtuka ta Botswana

2024-05-19 15:23:45 CMG Hausa

An kammala aikin gina cibiyar nazarin alluran rigakafin cututtuka ta kasar Botswana (BVI), wadda wani kamfanin Sin ya dauki nauyin ginawa, inda ake sa ran za ta tallafawa sana’ar kiwon shanu ta kasar.

Yayin da Andrew Madeswi, babban manajan cibiyar nazari ta BVI ke hira da wakilin CMG a kwanakin baya, ya ce yana godewa kamfanin kasar Sin da ya dauki nauyin aikin gina cibiyar, kan yadda ya samar da kayayyakin da Botswana ke bukata wajen zama mai samar da alluran rigakafin cututtuka ga daukacin kasashen Afirka.

Kiwon shanu wani ginshiki ne na tattalin arzikin kasar Botswana, inda fiye da rabin al'ummar kasar ke gudanar da ayyuka masu alaka da sana'ar. Sai dai a shekarun baya-bayan nan, aikin kiwon shanu na kasar na fuskantar matsalar barkewar annobar cututtuka. Don taimakawa kokarin shawo kan matsalar, wani kamfanin Sin ya dauki nauyin gina cibiyar nazari ta BVI a watan Yulin shekarar 2022. (Bello Wang)