logo

HAUSA

Taron ministocin harkokin wajen kasashe mambobin AES: Wani muhimmin matakin cimma kafa hadin gwiwar AES

2024-05-18 16:17:01 CMG Hausa

Ministocin harkokin wajen kasashe mambobin kungiyar yankin Sahel AES sun yi taro a ranar jiya Juma’a 17 ga watan Mayun shekarar 2024 a birnin Yamai, babban birnin kasar Nijar. Zaman taron da ya dora ga ci gaban tsarin shimfida makoma guda ta kasashen Burkina Faso, Mali da Nijar.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

 

A yayin wannan taro, ministocin harkokin wajen kasashen uku na AES da suka hada da Kamarako Jean Marie Traore na Burkina Faso, Abdoulaye Diop na Mali, da Bakary Yaou Sangare na Nijar, kewaye da kwararru, sun yi aikin nazari da amincewa da daftarin farko na shirin yarjejeniyar kafa kungiyar kasashen AES, da daftarin farko na dokokin gudanarwa na taron shugabannin kungiyar kasashen AES da kuma daftarin farko na sanarwar karshe ta taron shugabannin kasashen uku.

A dunkule wannan taro zai tantance niyya da dukufa na kasashe mambobin kungiyar AES na cimma wani sabon matsayin aiwatar da wannan hadaka, kamar yadda niyyar da aka dauka a yayin taron ministocin da ya gudana daga ranar 30 ga watan Nuwamba zuwa ranar 1 ga watan Disamban shekarar 2023 a birnin Bamako ta tanada.

Haka kuma, batutuwa da dama ne aka tattauna da ke da alaka da kalubalen tsaro, tattalin arziki da na siyasar duniya. Dukkan ministocin harkokin wajen uku sun jaddada niyyar kasashensu na ci gaba da hada karfi da karfe tare da la’akari da muhimman muradu da bukatun al’umominsu.

Daga karshe, ministocin sun nuna yabo bisa ga kokarin kasashen uku wajen taimakawa tabbatar da wannan hange mai cike da haske da shugabannin kasashen uku suka shata.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.