logo

HAUSA

Gwamnonin shiyyar arewa maso gabashin Najeriya sun fara taron duba makomar shiyyar da rikicin boko haram ya tagaiyara

2024-05-18 16:30:17 CMG Hausa

Gwamnonin jahohin dake shiyyar arewa maso gabashin Najeriya sun fara taro jiya Juma’a 17 ga wata a garin Bauchi, domin nazarin hanyoyin kyautata rayuwar al’umomin shiyyar da hare-haren ‘yan ta’addan Boko Haram ya daidaita tare kuma da farfado da tattalin arzikin yankin.

Taron karo na 10 wanda za a kammala shi a yammacin wannan rana ta asabar ya tabo batun ilimi da kiwon lafiya da kuma sauran ababen more rayuwa wanda mafiya yawan al’umomin yankin suka rasa sakamakon rashin cikakken kwanciyar hankali a jahohin dake shiyyar.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

 

Taron dai wanda gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ke jagoranta a matsayinsa na shugaban kungiyar gwamnonin jahohin arewa maso gabas ya bayyana takaicin yadda masu saka jari na gida da na kasashen waje ba sa samun kwarin gwiwar zuwa yankin domin saka jarinsu, duk kuwa da dimbin albarkatun da suke jibge a gaba daya jihohin da shiyyar.

A jawabinsa gwamnan jihar ta Borno ya ce wajibi ne gwamnonin jihohin dake shiyyar su hada karfi wajen farfado da tattalin arzikin shiyyar da kuma na rayuwar al’ummar dake zaune a shiyyar.

“Akwai bukatar mu karfafi gwiwar masu saka jari wajen zuwa domin saka jarinsu domin gaskata shirin na fitar da kayayyakin zuwa kasashen ketare, haka kuma a karkashin shirinmu na dakile hauhawar farashin kayayyakin abinci a shiyyar, muna bukatar mu mayar da hankali sosai wajen tabbatar da ganin shiyyar ta kasance mai dogaro da kanta.”

Shi ma gwamnan jihar Bauchi sanata Bala Muhamamd wanda shi ne mai masaukin baki shaidawa takwarorinsa ya yi a wajen taron cewa, “Babban makamin yaki da rashin zaman lafiya shi ne samar da ilimi da kuma aikin yi, ta haka ne al’ummar za su dauke hankalinsu daga shiga ayyukan ta’addanci.”

Dukkannin gwamnonin dai sun nuna amincewarsu a kan kudurorin da taron zai zartar wadanda za su taikamawa cigaban tattalin arzikin shiyyar da kuma walwalar al’umma. (Garba Abdullahi Bagwai)