logo

HAUSA

An yi kira da aiwatar da matakan samar da ilimi mai inganci a nahiyar Afirka

2024-05-18 16:11:53 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar Afirka ta AU da jami’ai daga bangaren kasar Sin, sun yi kira da a kara azama wajen aiwatar da matakan samar da ilimi mai inganci a sassan nahiyar Afirka, ta yadda hakan zai baiwa nahiyar damar cimma nasarar sauya salon tattalin arziki da zamantakewar al’ummunta.

An yi kiran ne a jiya Juma’a a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha, yayin taron tattaunawa na hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka game da raya ilimi.

Taron ya kuma mayar da hankali ga zakulo hanyoyin da kasar Sin za ta iya taimakawa nahiyar Afirka da su, ta yadda nahiyar za ta kai ga cimma manufar ci gaba mai dorewa ta MDD ko SDGs, da ma kudurorin dake cikin ajandar bunkasa nahiyar ta kungiyar AU na shekaru 50, wadanda ake fatan cimmawa nan zuwa shekarar 2063.

Da yake tsokaci yayin taron, kwamishinan AU mai lura da harkokin ilimi, kimiyya da fasaha, da kirkire-kirkire Mohammed Belhocine, ya ce ilimin fasahohi da na koyon sana’o’i, na taka muhimmiyar rawa ga cimma nasarar ajandar SDGs, da ta nahiyar Afirka ta nan zuwa shekarar 2063, don haka ya yi kira ga kasar Sin, da ta kara fadada bayar da horo a sassan Afirka, a fannonin koyon sana’o’in hannu da horaswa, kana ta horas da matasan nahiyar ilimomi, da sanin makamar aiki, da za su ba su damar baiwa kasashensu gudummawar raya tattalin arziki.

A nasa bangare kuwa, shugaban tawagar Sin a AU Hu Changchun, cewa ya yi a matsayinta na babbar abokiyar hadin gwiwar nahiyar Afirka bisa manyan tsare-tsare daga dukkanin fannoni, kasar Sin na matukar goyon bayan AU, a shirinta na cimma nasarar muradunta, tana kuma karfafa hadin gwiwa da nahiyar a fannin raya ilimi, da bangaren samar da kwarewa.   (Saminu Alhassan)