Ribar gajiyar masana’antun ba da hidimar tauraron dan Adam na ba da jagorancin taswira na Sin ta karu da 7% a bara
2024-05-18 21:24:25 CMG Hausa
Jimillar ribar gajiyar sashen masana’antun ba da hidimar tauraron dan Adam, na ba da jagorancin taswira na Sin ta karu da kaso 7 bisa dari a shekarar 2023.
Wata takardar bayanai da aka wallafa a Asabar din nan ta bayyana hakan, tare da bayyana kimar sashen kan kudin Sin yuan biliyan 536.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 74.2 a shekara ta bara, wanda hakan ke nuni ga karuwar kaso 7.09 bisa dari sama da na shekarar 2022.
Kungiyar masu lura da tsarin taurarin dan Adam na hidimar ba da jagorancin taswira ko GNSS, da hidimomin ayyana wurare ko LBS ta kasar Sin ce ta fitar da takardar bayanan ta shekarar bana, wadda ke kunshe da irin ci gaban da kasar Sin ta samu a fannin raya masana’antar ba da hidimomin tauraron dan Adam, mai ba da jagorancin taswira da hidimomin fayyace wurare.
A cewar shugaban kungiyar Yu Xiancheng, ya zuwa karshen shekarar ta bara, adadin kamfanoni, da cibiyoyi dake samar da hidimomi a wannan fanni a kasar Sin ya kai kusa 20,000, yayin da adadin mutanen dake aiki a sashen ya kai kusan miliyan guda. Kaza lika an sanya irin wadannan kamfanoni 90, a jerin kamfanoni masu hannayen jari mallakin al’umma. (Saminu Alhassan)