logo

HAUSA

Ministan harkokin wajen Sin ya zanta da takwaransa na Tanzania

2024-05-17 19:45:32 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya zanta da ministan kula da harkokin waje, da harkokin hadin gwiwa da gabashin Afirka na kasar Tanzania January Yusuf Makamba, a yau Juma’a a nan birnin Beijing.

Yayin zantawar tasu, Wang ya ce, har kullum alakar Sin da Tanzania na sahun gaba, cikin dangantakar Sin da kasashen Afirka, inda sassan biyu suka shafe sama da shekaru 60 suna cudanyar diflomasiyya, lamarin da ya aza wani kyakkyawan misali na dangantakar kasashe masu tasowa, dake fatan karfafa goyon baya da taimakawa juna.

Wang ya kara da cewa, Sin na jinjinawa Tanzania, bisa goyon baya mai daraja na tsawon lokaci, game da batutuwan da suka shafi muhimman  moriyarta, kuma Sin a shirye take ta ci gaba da goyon bayan Tanzania a fannin kare ikon mulkin kai, da tsaro da ci gaban moriyarta, kaza lika da lalubo turbar kashin kai ta samun bunkasuwa mafi dacewa da yanayin da kasar ke ciki.

A nasa bangare kuwa, mista Makamba, ya ce har kullum kasashen biyu suna amincewa da goyon bayan juna tun kafuwar huldar diflomasiyyarsu shekaru 60 da suka gabata. Daga nan sai ya bayyana fatan Tanzania, na ci gaba da musayar kwarewa a fannonin jagoranci, da zurfafa hadin gwiwar cimma moriya tare a fannoni daban daban, kana da aiki kut da kut tare da Sin, a harkokin kasa da kasa da na shiyyoyi.   (Saminu Alhassan)