Wang Yi ya jajantawa takwaransa na Afghanistan sakamakon ambaliyar ruwa da ta auku a kasar
2024-05-17 14:59:46 CMG Hausa
Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya mika sakon ta’aziyya ga mukaddashin ministan harkokin waje na wucin gadi na kasar Afghanistan Amir Khan Muttaqi, kan bala’in ambaliyar ruwa mai tsanani dake addabar kasar.
Wang Yi wanda ya bayyana hakan a jiya Alhamis, ya ce yana mai bakin ciki ga asarar rayuka, da dukiyoyin da ambaliyar ruwan ke haddasawa a wasu yankuna daban-daban na kasar. Daga nan sai ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da alhini ga iyalan mamatan da wadanda suka ji raunuka. Ya kuma yi imanin cewa, al’ummar kasar za su shawo kan bala’in, da komawa yanayin zaman rayuwarsu yadda ya kamata cikin kankanin lokaci.
Ban da wannan kuma, ya ce Sin za ta ba da taimako gwargwadon karfinta bisa bukatun kasar ta Afghanistan. (Amina Xu)