logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya murnar bude bikin baje kolin kayayyakin Sin da Rasha karo na 8

2024-05-17 14:43:25 CMG Hausa

 

A yau Juma’a, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya mika sakon taya murnar bude bikin baje kolin kayayyakin Sin da Rasha karo na 8.

Cikin sakon nasa, Xi Jinping ya bayyana bikin a matsayin wani dandalin ingiza cinikayyar bangarorin biyu, bayan kokarin da aka yi a shekarun baya bayan nan da suka gabata. Ya kuma yi fatan sassa masu ruwa da tsaki za su yi amfani da zarafi mai kyau na wannan karo, don kara tuntubar juna, da more damammaki, da kuma taka rawar gani wajen gaggauta hadin gwiwa, da cin gajiyar bangarorin biyu, ta yadda za a samar da sabon karfin raya huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare, a dukkan fannoni a sabon zamani.

Ma’aikatar kasuwancin kasar Sin da gwamnatin lardin Heilongjiang, da hukumar raya tattalin arzikin Rasha, da ma’aikatar masana’antu da ciniki ta Rasha ne suka yi hadin gwiwar shirya bikin na wannan karo, bisa taken “Hadin kai da amincewa da juna, da kawowa juna alheri”. An kuma gudanar da baje kolin ne a birnin Harbin, fadar mulkin lardin Heilongjiang. (Amina Xu)