logo

HAUSA

Taron koli karo na 33 na kungiyar AL ya yi kira da a gaggauta shirin kafa kasashen Palasdinu da Isra’ila

2024-05-17 14:57:08 CMG Hausa

 

Da yammacin Jiya Alhamis ne aka rufe taron koli karo na 33, na kungiyar kasashen Larabawa wato AL, a Manama fadar mulkin kasar Bahrain. An kuma gabatar da sanarwar Bahrain, inda aka yi kira da a gaggauta tabbatar da aldaci, da zaman lafiya a dukkanin fannoni tsakanin Palasdinu da Isra’ila, bisa manufar kafa kasashe biyu.

A cikin sanarwar, mahalarta taron sun nuna goyon baya ga shawarwarin da shugaban Palasdinu Mahmoud Abbas ya gabatar, wato gudanar da taron wanzar da zaman lafiya a duniya, inda ya yi kira da a dauki matakai ba tare da ja da baya ba don tabbatar da manufar.

Baya ga haka, sanarwa ta yi kira da a jibge sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD a yankunan Palasdinu da aka mamaye, don tabbatar da nasarar manufar yadda ya kamata. (Amina Xu)