Sin na maraba da kamfanonin kasa da kasa da su zuba jari da aiwatar da hada-hada a kasar
2024-05-17 20:40:20 CMG Hausa
Wasu rahotanni na cewa, kwamitin kungiyar tarayyar Turai ta EU, ya daga hasashen bunkasar tattalin arzikin kasar Sin zuwa kashi 4.8 bisa dari a bana, a cikin rahoton hasashen tattalin arziki na lokacin bazarar shekarar nan ta 2024.
Game da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, tun daga shekarar bana, farfadowar tattalin arzikin Sin ya sanya sassan kasa da kasa na ta nuna kyakkyawar makoma ga kasar Sin. A daya hannun kuma, Sin din tana maraba da kamfanonin kasa da kasa, da su ci gaba da zuba jari, da aiwatar da hada-hada a kasar Sin.
Game da ra’ayin da kakakin ma’aikatar harkokin wajen Amurka ya bayyana game da huldar dake tsakanin Sin da Turai kuwa, Wang Wenbin ya bayyana cewa, Sin ta kalubalanci Amurka, da ta daina yada jita-jita kan kasar Sin, da kawo cikas ga raya huldar dake tsakanin Sin da Turai, da kuma rura wuta. Maimakon haka, kamata ya yi ta dauki matakai na warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa.
Ban da wannan kuma, Wang Wenbin ya ce, Sin tana son yin kokari tare da kasashen Larabawa, wajen ci gaba da yada tunanin sada zumunta a tsakaninsu, da raya makomar bai daya mai inganci, da kuma samar da gudummawa, ta raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama. (Zainab Zhang)