logo

HAUSA

OIC: Allurar rigafin HPV tana da tasirin gaske wajen maganin kamuwa da ciwon kansar mahaifa

2024-05-17 09:15:43 CMG Hausa

Uwargidan shugaban tarayyar Najeriya Sanata Oluremi Tinubu ta tabbatarwa ’yan kasar cewa allurar rigakafi na HPV tana da ingancin gaske wajen kare kamuwa da ciwon dajin bakin mahaifa ga ’yan mata.

Ta tabbatar da hakan ne jiya Alhamis 16 ga wata a birnin Abuja yayin babban taron karawa juna sani da membonin kungiyar kasashe musulmi ta duniya (IOC) suka shirya domin wayar da kai a game da illar ciwon kansar mahaifa. Ta ce, babban burinta dai shi ne a rage karuwar cutar a tsakanin mata ta hanyar kyautata hanyoyin rigakafinta.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Uwargidan shugaban na tarayyar Najeriya ta lasafto wasu daga cikin tsare-tsaren da gwamnatin kasar ta bullo da su domin dai maganin cutar kansar mahaifa a Najeriya, wadanda suka hada da kara adadin kaso da ake warewa bangaren kiwon lafiya a kasafin kudi na bana na 2024, tare kuma da fadada cibiyoyin lura da masu dauke da cutar kansar.

Ta ci gaba da cewa, daga cikin fa’idoji da kuma alfanun wannan babban taro na kungiyar OIC shi ne, musayar ra’ayoyi da kuma shawarwari a kan yadda za a samar da kudade domin amfani da su wajen aikin yakar cutar kansar musamman dai ma kansar mama da ta mahaifa, kuma za a iya cimma hakan ne ta hanyar hanzartar gano cutar da wuri kafin ta yi karfi a jikin mace.

“Ofishi na zai ci gaba da aiki tare da dukkannin masu ruwa da tsaki domin shawo kan kalubalen da ake fuskanta wajen jinkirin gano cutar ta kansa a kasa baki daya, tare kuma da kara inganta tsarin lura da masu fama da wannan lalura.”

Tsididdigar rahoton cibiyoyin tattara bayanan masu dauke da cutar kansar a Najeriya tare da hadin gwiwa da kungiyar Globocan sun nuna cewa a tsakanin shekara guda da ta gabata, an samu sabbin mutanen da suke dauke da cutar kansar mahaifa har su dubu 127 da 763, haka kuma rahoton ya nuna cewa mutane dubu 79 ne da 542 suka mutu daga cikin wannan adadi. (Garba Abdullahi Bagwai)