logo

HAUSA

Amurka za ta samarwa Ukraine tallafin kudi har dala biliyan 2 domin ayyukan soji

2024-05-17 14:17:52 CMG Hausa

Kamfanin dillancin labarai na Interfax-Ukraine ya rawaito cewa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, wanda ke ziyara a kasar Ukraine, ya sanar da cewa, Amurka za ta samar da gudummawar soja da ta kai dalar Amurka biliyan 2 ga Ukraine.

Blinken ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka yi a ranar Laraba, inda ya kara da cewa, za a yi amfani da wadannan kudi ne wajen samar da makamai ga Ukraine, da zuba jari ga masana’antun samar da kayayyakin tsaron kasa ta kasar, da nufin kara karfin Ukraine na kera na’urorin tsaron kasa.

An ce kudin na daga cikin agajin soji da na tattalin arziki kusan dala biliyan 61, wanda Amurka ta amince ta baiwa Ukraine a watan jiya, da ma "kudin tallafin soja na kasar waje", wanda a baya Amurkan ba ta bayyana wace kasa za ta baiwa ba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)