logo

HAUSA

Kasashen Afrika sun ba da shawarwarin tinkarar matsalar kiwon lafiya cikin gaggawa

2024-05-16 14:36:38 CMG Hausa

 

A jiya Laraba ne kasashen Afrika, suka gabatar da shawarwarin tinkarar matsalar kiwon lafiya cikin gaggawa, sakamakon yadda lamarin ke kara tsananta saboda sauyin yanayi.

Shirin tinkarar matsalar kiwon lafiya cikin gaggawa na gabas, da kudancin Afrika wato HEPRR, wanda darajarsa ta kai dalar biliyan 1, zai canja matakan dauka don magance matsalar.

Game da hakan, sakantariyar ma’aikatar kiwon lafiya a gwamnatin kasar Kenya Susan Nakhumicha, ta ce shirin wanda za a aiwatar a nahiyar Afrika, bisa taimakon bankin duniya, zai kara karfin Afrika na tinkarar cututtukan annoba, da sauran kalubalolin kiwon lafiya.

Susan Nakhumicha, ta kara da cewa, cutar Ebola, da zazzabin Marburg, da shawara, da zazzabin chikungunya da sauransu, sun addabi hukumomin kiwon lafiya, tare da haifar da cikas ga ingantattun hidimomin da hukumomin ke iya bayarwa.

Daga nan sai jami’ar ta shawarci gwamnatocin kasa da kasa, da su kara karfin binciken lafiyar al’umma, da samar da magunguna da allurar rigakafi, da kuma inganta karfin tinkarar sauyin yanayi, ta yadda za su magance matsalar. (Amina Xu)