Kamaru ta sanar da jerin ‘yan wasan ta 31 da za su buga mata wasannin neman gurbin gasar cin kofin duniya
2024-05-16 20:36:01 CMG Hausa
Mahukuntan kwallon kafa a kasar Kamaru, sun fitar da jerin sunayen ‘yan wasan kwallo su 31, wadanda za su bugawa kasar wasannin neman gurbin buga gasar cin kofin kwallon kafa na duniya wanda hukumar FIFA ke shiryawa, wanda za a buga a shekarar 2026. Mahukuntan sun kuma gabatar da sabon babban kocin kungiyar Marc Brys.
Gabanin wasan horo na farko da ya yi tare da ‘yan wasan tawagar kasar, Marc Brys dan asalin kasar Belgium, ya kira sababbin ‘yan wasa 7 da suka hada da Carlos Baleba, James Eto'o, Yvan Dibango, Raoul Danzabe, Guy Kilama, Nchindo John Bosco, da kuma Jules Armand Kooh.
Kaza lika, ‘yan wasan kungiyar da suka jima ba su bugawa Kamaru kwallo ba, irin su Eric Maxim Chopou-Moting, Fai Collins, Bryan Mbeumo, Michael Ngadeu-Ngadjui da Christian Mougang Bassogog, a wannan karon sabon kocin ya gayyato su.
Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a birnin Yaounde, Brys ya ce yana fatan yin aiki tare da ‘yan wasa masu karsashin buga wasa da kaunar kasar su. Ya ce "Da yawa daga ‘yan wasan da na kira suna kan ganiyar su. Mun duba ‘yan wasa masu hazaka cikin wadanda ba sanannu ba ne".
Yanzu haka dai Kamaru za ta buga muhimman wasanni biyu na neman gurbin gasar ta cin kofin duniya a watan Yuni, tsakanin ta da Cape Verde da kuma Angola.
Neymar ba zai bugawa Brazil wasannin cin kofin Copa America ba
Tauraron kwallon kafar kasar Brazil Neymar, ba zai bugawa kungiyar kasarsa wasannin cin kofin Copa America ba, sakamakon ci gaba da jinyar da yake yi ta matsanancin ciwon gwiwa.
A cewar hukumar kwallon kafar Brazil, Neymar mai shekaru 32 bai buga wani wasa ba, tun bayan da ya ji rauni a gwiwarsa ta hagu a cikin watan Oktoba, inda tun a lokacin aka yi hasashen da wuya ya samu bugawa Brazil din wasannin Copa America, wanda za a fara bugawa tun daga ranar 20 ga watan Yuni.
Baya ga Neymar, dan wasan tsakiyar Manchester United Casemiro, da dan wasan gaba na Tottenham Hotspur Richarlison, su ma ba za su samu buga wasannin gasar ba, saboda rashin haskakawa, da kuma rauni da suke fama da su tun daga kulaflikan da suke bugawa wasa.
Kamar dai yadda aka yi tsammani, manajan kungiyar Dorival Junior, ya ayyana sunan matashin dan wasan Palmeiras mai shirin tafiya Real Madrid wato Endrick, cikin jerin ‘yan wasa 23 da Brazil din za ta tafi da su wannan gasa.
Endrick zai tafi Real Madrid da zarar ya cika shekaru 18 a watan Yuli, kuma tuni ya ci wa Brazil kwallo 1 da nema, yayin wasan da suka buga da Ingila a filin Wembley, kana ya ciwa Brazil din kwallo 1 a wasan da aka tashin kunnen doki 2 da 2 da Sifaniya, a filin wasa na Santiago Bernabeu cikin watan Maris.
Brazil za ta buga wasan farko a gasar Copa America da kasar Costa Rica a birnin Los Angeles a ranar 24 ga watan Yuni, kana za ta hadu da Paraguay da Colombia a sauran wasannin rukuni.
Mbappe ya bayyana shirin ban kwana da PSG
Kylian Mbappe, ya tabbatar da shirinsa na ban kwana da kungiyar Paris Saint-Germain, bayan shafe shekaru 7 yana bugawa kwallo a karshen kakar bana, ba tare da ya bayyana inda zai koma ba.
To sai dai kafofin watsa labarai daban daban na cewa Mbappe na shirin komawa Real Madrid ne, bayan kammala kakar wasan da ake bugawa.
A ta bakin sa, cikin wani sakon bidiyo da ya wallafa a kafar sada zumunta, Mbappe ya ce "Ina son na sanar da ku baki daya, cewa wannan ce shekarata ta karshe a Paris Saint-Germain. Ba zan tsawaita kwangila ta ba, kuma wasannin da nake bugawa kungiyar za su kawo karshe nan da ‘yan makwanni kadan masu zuwa. Zan bugawa PSG wasan karshe a wasan da za mu buga a Parc des Princes".
Tun a shekartar 2017 ne dan wasan dan asalin Faransa ya fara taka leda a PSG, bayan da kungiyar Monaco ta bayar da shi bashi, kana daga baya aka yi cinikinsa kan kudi euro miliyan 180.
Cikin shekaru 7 da Mbappe ya shafe a PSG, ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofuna 6, da kofunan gasannin Faransa 3, inda ya buga wasanni 306 da cin kwallaye 255, tare da zama dan kwallo mafi ciwa kungiyar kwallaye a dukkanin tarihin ta.
Dan wasan mai shekaru 26 a yanzu, ya ce "Abu ne mai matukar taba zuciya, barin kungiya da na shafe shekaru da dama ina bugawa wasa. Wannan dama ce babba da kungiyar ta ba ni, a matsayin ta na daya daga kungiyoyi mafiya tashe a duniya. Kungiyar ce ta bani zarafin kawowa inda nake, na dandana yanayin kungiya mai fuskantar matukar matsin lamba, na samu ci gaba a matsayi na na dan wasa, inda na fafata tare da manyan taurarin wasa a tarihi, ciki har da mafiya daukaka a harkar kwallo. Abu ne mai wahala sanar da wannan aniya. Amma ina ga ya zama dole, domin ina bukatar sabon kalubale, bayan shekaru 7".
Tuni dai PSG ta lashe gasar Ligue 1 ta kakar bana, ta kuma kai ga wasan karshe na cin kofin “French Cup”, inda za ta buga wasan na karshe da Lyon a ranar 25 ga watan Mayu. Sai dai kuma a gasar cin kofin zakarun turai, inda kungiyar ta so nuna tasirin ta, a bana ta yi gamo da rashin nasara a wasan kusa da na karshe, bayan da Borussia Dortmund ta Jamus ta yi waje da ita.
‘Yan wasan tseren gudun mita 100 na kasar Ghana sun samu gurbin zuwa gasar Olympic ta Faransa
‘Yan wasan tseren gudu da mika sanda, ajin mita 100 na kasar Ghana su hudu, sun yi nasarar samun gurbin shiga gasar Olympic ta Paris ta bana, bayan da suka nuna bajimta a gasar wasannin motsa jiki ta duniya a Bahamas.
Da fari dai ‘yan wasan sun gamu da kalubale a tseren farko da suka yi, inda suka kammala a matsayi na 8, sakamakon faduwar da sandar su ta yi a zagayen na farko, lokacin da suke kokarin sauya hannu, to amma daga baya sun samu nasara a zagaye na biyu.
‘Yan wasan hudu, Ibrahim Fuseini, da Isaac Botsio, da Benjamin Azamati, da kuma Joseph Paul Amoah, wanda ke rike da lambar zinari ta gasar gudun mita 200, ta gasar wasannin kasashen Afirka da ta gabata, a wannan karo a gasar Bahamas, sun kammala tseren mita 100 a matsayi na biyu, bayan kammala tseren cikin dakika 38.29. Kwazon da suka yi ya tabbatar da nasarar da suka samu ta kara kyautata tsere tare, bayan ga gurbin shiga gasar Olympic ta Paris da suka samu.
A wannan tsere mai kayatarwa, ‘yan wasan na Ghana sun zarce takwarorin su na tawagar Najeriya, wadanda su ma suka samu gurbin zuwa gasar ta Olympic, bayan kammala tsere cikin dakika 38.57, a matsayi na biyu na zagayen tseren.