logo

HAUSA

Sin ta tsara muhimman ayyukan zamanantar da kauyuka

2024-05-16 14:26:06 CMG Hausa

Wasu hukumomin kasar Sin sun fitar da shawarar hadin gwiwa ta aiwatar da muhimman ayyukan gina kauyuka na zamani har 28 a shekarar bana.

Hukumomi masu nasaba da aikin, sun gabatar da shawarar ne a jiya Laraba, inda suka jaddada cewa, ya kamata a inganta zamanantar da aikin noma, da kauyuka ta fasahohin sadarwa, da inganta aikin noma mai inganci, da gina kauyuka masu dacewa da aiki da rayuwar al’umma, da kuma kara ingancin rayuwar manoma. 

Muhimman ayyukan suna da bangarori guda tara, wadanda suke dora muhimmanci kan inganta aikin noma mai amfani da fasahohin zamani, da sanya karin kuzari ga tattalin arziki na zamani a gundumomi, da farfado da al’adar cin gajiyar fasahohin dijital a kauyuka, da kyautata tsarin gudanar da fasahohin dijital na kauyuka da sauransu.

Bugu da kari, takardar da aka fitar mai nasaba da aikin, ta fitar da makasudi a jere. Inda ta yi hasashen cewa, ya zuwa karshen shekarar nan ta 2024, yawan masu amfani da layin sadarwa a yankunan karkara za su haura miliyan 200, kuma sadarwar intanet a yankunan karkara za ta karu da kashi 2 cikin dari, sannan za a kai ga tallata kayayyakin amfanin gona kan hanyoyin sadarwar intanet, wadanda darajar su za ta zarce yuan biliyan 630, kimanin dalar Amurka biliyan 88.67. (Safiyah Ma)