logo

HAUSA

Mutane hudu sun rasu yayin hari da ‘yan aware suka kaddamar a Kamaru

2024-05-16 14:48:43 CMG Hausa

Jami'an tsaro biyu, da fararen hula biyu ne aka tabbatar da rasuwar su, yayin wani hari da 'yan awaren kasar Kamaru suka kaddamar a yankin dake amfani da Turanci, na arewa maso yammacin kasar dake fama da tashe tashen hankula, kamar dai yadda majiyoyin tsaro suka sanar a jiya Laraba.

Wani babban jami'in tsaro, ya ce 'yan awaren sun kai wa jami'an tsaron Kamaru biyu harin kwanton-bauna ne a yankin Bambi dake yankin, a daren ranar Talata.

Jami'in da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida wa ‘yan jarida na kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, sojojin sun sha barasa a wata mashaya, suna kuma shirin fita ne 'yan awaren dake boye suka bude musu wuta, inda nan take suka harbe sojoji biyu, tare da mai mashayar, da wata mace daya. Jami’in ya kara da cewa, wata mace mai shekarun 26, ita ma ta samu rauni yayin harbe harben, kuma ana mata jinya a asibiti.

A daidai lokacin da Kamaru ke shirin gudanar da bukukuwan ranar kafuwar kasa ranar 20 ga watan nan na Mayu, ‘yan aware masu dauke da makamai, na kara kaddamar da hare-hare a yankunan dake amfani da Turanci, dake arewa maso yamma, da kudu maso yammacin kasar. (Safiyah Ma)