logo

HAUSA

Xi Jinping ya mika sakon murnar kaddamar da taron koli na LAS karo na 33

2024-05-16 21:03:59 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sako ga sarkin kasar Bahrain, kuma shugaban majalissar kawancen kasashen Larabawa wato LAS na wannan karo Hamad Bin Issa Al Khalifa, don murnar kaddamar da taron koli na majalisar karo na 33 a birnin Manama.

A cikin sakon, shugaba Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a shekarun baya-bayan nan, an samu babban canji a duniya, kuma kasashen Larabawa sun kiyaye ‘yancin kansu, da sa kaimi ga samun bunkasuwa da farfadowar al’ummunsu, da tabbatar da adalci da zaman lafiya a yankinsu, kana sun taka muhimmiyar rawar raya hadin gwiwa, da tabbatar da samun moriya tare a tsakanin kasashe maso tasowa.

Shugaba Xi ya jaddada cewa, Sin tana son yin kokari tare da kasashen Larabawa, wajen ci gaba da yada tunanin sada zumunta a tsakaninsu, da raya makomar bai daya mai inganci, da kuma samar da gudummawa wajen raya al’umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama. (Zainab Zhang)