logo

HAUSA

Xi da Putin sun halarci bikin kaddamar da shekarar al’adun Sin da Rasha

2024-05-16 19:52:20 CMG Hausa

 

A yau Alhamis shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, sun halarci bikin kaddamar da shekarar al’adun Sin da Rasha, da bikin kide-kide da raye-raye na musamman, wanda aka shirya a birnin Beijing, domin murna cika shekaru 75 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Rasha.  

Da farko shugaba Xi ya gabatar da jawabi, inda ya bayyana cewa, rungumar shekarar juna mai take daban daban, ta zama wata al’ada mai kyau a salon musayar al’adun Sin da Rasha, kana hakan na nuna halin musamman, da muhimmanci cikin tarihin bunkasar dangantakar sassan biyu, wadda ta samu karbuwa matuka tsakanin al’ummun kasashen biyu.

A bana, sassan biyu za su gudanar da ayyukan musayar al’adu masu kayatarwa, don zurfafa hadin gwiwar musayar al’adunsu, da aiki tare, wajen bude sabon babin ingiza musayar al’adu tsakanin Sin da Rasha.

A nasa bangare kuwa, shugaba Putin ya bayyana cikin jawabinsa cewa, bisa manufar martaba juna, da daidaito da amincewa juna, kasashen biyu sun ingiza ci gaban kasashensu, kuma al’ummunsu sun ci gajiya, kana sun samar da misali na alakar kasa da kasa.

Ya ce, Rasha a shirye take ta zurfafa musayar al’adu da ta al’ummu da Sin, ta yadda za su kara bunkasa fahimtar juna, da yayata manufar kara daga matsayin hadin gwiwar sassan biyu yadda ya kamata. (Saminu Alhassan)