Sin ta musunta zargin da Amurka ta yi mata game da samar da abubuwan kera makamai ga Rasha
2024-05-16 20:10:24 CMG Hausa
Game da zargin da kasar Amurka ta yiwa kasar Sin, cewa tana samarwa kasar Rasha abubuwan kera makamai, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, Sin ta musanta wannan zargi.
Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin na yin taka tsantsan a fannin fitar da kayayyakin soja, da daukar tsauraran matakai kan kayayyaki masu nasaba da aikin soja da na al’umma, ciki har da fitar da jiragen sama marasa matuka dake ayyukan farar hula.
Sai dai a hannu guda kowa ya san yadda Amurka ta samar da gudummawar kayayyakin aikin soja ga kasar Ukraine, yayin da kuma take zargin mu’amalar tattalin arziki da cinikayya dake gudana tsakanin Sin da Rasha, lamarin da ya zamo ma’auni biyu da Amurka take dauka, don haka ta gaza sauke alhakin dake kanta.
Ban da wannan kuma, game da yadda Isra’ila ta ki amincewa da kudurin baiwa bangaren Falasdinu iznin halartar ayyukan MDD, wanda babban taron MDD ya zartas, Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, ya kamata a aiwatar da shirin shimfida zaman lafiya a tsakanin Isra’ila da Falasdinu, da nuna goyon baya ga Falasdinu, don ta zama mambar MDD a hukumance, da kaiwa ga cimma zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu, ta yadda za a taimaka wajen shawo kan rikicin dake tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)