logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Rasha sun tattauna da juna

2024-05-16 14:27:32 CMG Hausa

 

Da safiyar yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya tattauna da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, wanda ke ziyarar aiki a nan kasar Sin.

Yayin ganawar su a nan Beijing, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, muhimmin aikin bunkasa huldar kasashen biyu a bana, shi ne murnar cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyyar kasashen biyu. Ya ce Sin da Rasha sun nuna misali na kafa huldar mutunta juna, da nuna sahihanci, da zaman tare cikin lumana, da kuma hadin gwiwa tsakanin manyan kasashen dake makwabtaka da juna.

Shugaba Xi ya ce a cikin shekarun da suka gabata, ya gana da Vladimir Puti kimani sau 40, kuma ko da yaushe suna ci gaba da mu’ammala da tuntubar juna, matakin da ya ba da jagorancin gudanar da manyan tsare-tsaren bunkasuwar huldar kasashen biyu.

A cewarsa, bunkasuwar huldar kasashen biyu mai karko, ta dace da muradun jama’ar kasashen biyu, kuma za ta yi amfani wajen tabbatar da zaman lafiya da karko, da wadatar yanki, da ma duk fadin duniya baki daya. Har ila yau, kasar Sin na fatan ci gaba da hadin kai da kasar Rasha a nan gaba, a matsayin su na makwabta, kuma abokan juna masu dakon zumunci, kana za su ingiza huldar al’ummar kasashen biyu har abada, da ma hadin gwiwarsu wajen tabbatar da bunkasuwar kasashen biyu, da kiyaye zaman lafiya da adalci a duniya. (Amina Xu)