logo

HAUSA

Amurka za ta lashe amanta game da karin harajin rashin adalci da ta bugawa kasar Sin

2024-05-16 15:26:58 CMG Hausa

 

A ranar Talata 14 ga watan nan ne gwamnatin Amurka, ta sanar da buga karin haraji kan wasu hajojin dake shiga kasar daga kasar Sin, matakin da ya gamu da nuna rashin jin dadi, da adawa daga al’ummar duniya. 

Amurka ta rika siyasantar da batun ciniki, wanda hakan ya keta hurumin hada-hadar cinikayyar sassan biyu, kuma zai illata bunkasuwar harkoki masu alaka, daga karshe dai Amurka za ta lashe amanta tare da gamu da babbar illa.

Hajojin da gwamnatin Amurka ta dorawa matsin lamba a wannan karo sun shafi musamman na fannin amfani da makamashi mai tsabta. Sakamakon haka muna iya ganin cewa, zargin da wasu manyan jami’an Amurka suka yi, cewar wai yawan hajoji masu aiki da makamashi mai tsabta da Sin ke samarwa sun wuce misali, hujja ce kawai ta neman buga karin haraji.

To ko mene ne dalili? Manazarta na ganin cewa, a wani bangare, Amurka ta gaza samun karfin takara a wannan bangare, shi ya sa ’yan siyasar ta suke yunkurin dakile hada-hadar Sin mai fifiko bisa manufar kariyar cinikayya.

A wani bangare na daban kuwa, matakin ya kasance wani wasan kwaikwayo na siyasa, duba da cewa, za a gudanar da babban zaben Amurka a bana. Amma, a halin yanzu ana fuskantar hauhawar farashi, da gibin kasafin kudi mai tsanani da dai sauran kalubaloli, don haka dora laifi kan wasu, mataki ne da ’yan siyasar kasar Amurka suka dade suna aiwatarwa.

Sana’ar samar da hajoji masu aiki da makamashi mai tsabta ta kasar Sin, ba ma kawai ta samarwa duniya isassun hajoji ba ne, har ma ta sassauta hauhawar farashinsu a duniya, kuma ta taka rawar gani wajen tinkarar sauyin yanayi, da karkata zuwa hanyar samun bunkasuwa ba tare da bata muhalli ba. Don haka dai yunkurin Amurka na dakile kasar Sin ba zai hana ci gabanta ba, sai dai kawai ya fayyace rashin hangen nesa, da kasancewa mai keta ka’idar duniya. (Amina Xu)