Shugabannin Sin da Rasha sun fitar da sanarwar hadin gwiwa
2024-05-16 14:54:24 CMG Hausa
A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya zanta da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, wanda yake ziyarar aiki a Sin, a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Yayin zantawar, shugabannin kasashen biyu sun sa hannu, da kuma gabatar da wata hadaddiyar sanarwa, game da karfafa dangantakar abokantakar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, a sabon zamani, tsakanin janhuriyar jama’ar kasar Sin da tarayyar Rasha, yayin da ake cika shekaru 75 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin kasahsen biyu. (Safiyah Ma)