logo

HAUSA

An wallafa makalar Xi Jinping mai take “Zurfafa kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje da inganta aikin zamanintarwa irin na kasar Sin”

2024-05-15 16:05:58 CMG Hausa

 Jiya Talata, Mujallar “Neman Gaskiya” ta wallafa wani muhimmin makalar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya rubuta mai taken “Zurfafa kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje domin kara sa kaimi wajen bunkasa aikin zamanintar wa irin na kasar Sin”.

Makalar ta nanata cewa, tsarin yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga waje muhimmin mataki ne da Sin take bi a halin yanzu don zamanintar da kanta, kuma kamata ya yi a tsai da babban shirin zurfafa yin kwaskarima a sabon mataki, ta yadda za a samar da karfi mai inganci ga gaggauta samun ingantaccen bunkasuwa da zamanintarwa iri na kaasr Sin. (Amina Xu)