logo

HAUSA

Kawancen sojin Amurka da Birtaniya ya gudanar da karin luguden wuta 4 a filin jirgin saman Hodeidah na Yemen

2024-05-15 11:33:36 CMG Hausa

Jiragen yakin kawacen sojin ruwan Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare 4 ta sama a filin jirgin saman birnin Hodeidah na Yemen dake bakin tekun Maliya, wanda ke karkashin ikon kungiyar Houthi.

Har yanzu kawacen sojin bai yi tsokaci kan sabbin hare-haren ba, amma da farko a wannan rana, rundunar sojin Amurka ta wallafa a shafin X cewa, dakarunta sun harbo tare da lalata wasu jirage marasa matuki da makamai masu linzami na lalata jiragen ruwa da aka harba daga yankin Yemen dake hannun kungiyar Houthi, wadda ke samun goyon bayan Iran.

Sanarwar ta kara da cewa, ba a samu jikkatar mutane ko lalacewar kayayyaki ko jiragen ruwa daga rundunar kawacen na Amurka ba.

Haka kuma, a ranar Litinin, kawancen sojin ya ce ya kai wani hari ta sama kan wannan filin jirgin sama, wanda mayakan Houthi ke amfani da shi a matsayin sansani.(Fa’iza Mustapha)