logo

HAUSA

Xi Ya Yi Kira Da A Karfafa Azamar Yayatawa Da Kare Babbar Ganuwar Kasar Sin

2024-05-15 19:40:26 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi kira da a kara azamar yayata Babbar Ganuwar kasar Sin, ta yadda karin mutane za su san ta, kana a kara adadin mutanen dake shiga ayyukan kare ganuwar, ta yadda za a mika gadonta zuwa zuri’o’i na gaba.

Shugaba Xi ya yi tsokacin ne cikin wasikar martani da ya aike ga mazauna kauyen dake kusa da yankin Badaling na Babbar Ganuwar dake arewacin wajen birnin Beijing a jiya Talata.   (Saminu Alhassan)