logo

HAUSA

Luguden wutan Isra'ila ya yi sanadin mutuwar mutane 40 a tsakiyar Gaza

2024-05-15 10:44:10 CMG Hausa

Mutane a kalla 40 sun mutu yayin da wasu suka jikkata, sanadiyyar harin da Isra'ila ta kai a tsakar daren ranar Litinin, kan sansanin 'yan gudun hijira na Nuseirat dake yankin tsakiyar Zirin Gaza.

Wani rahoton gidan talabijin na Palasdinu ya ruwaito cewa, jiragen yakin Isra'ila sun kai hari kan gine-ginen iyalin Karaja dake kudancin sansanin Nuseirat, kuma yara suna cikin wadanda harin ya rutsa da su.

Rundunar sojin Isra'ila ta sha kai hare-hare kan sansanin na Nuseirat. A baya bayan nan a karshen Afrilu, jiragen yakinta sun kai hare haren makamai masu linzami kan wani gida dake sansanin, lamarin da ya yi sanadin rayukan Palasdinawa 9, ciki har da yara 4, tare da jikkata wasu 30.

A cewar hukumomin lafiya na Gaza, adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa Zirin Gaza, ya zarce 35,000. (Fa'iza Mustapha)