logo

HAUSA

Wang Yi: Kokarin Amurka Na Murkushe Cinikayya Da Fasahohin Sin Salo Ne Na Danniya

2024-05-15 20:25:08 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce Amurka na ta aiwatar da matakan keta, da nufin murkushe harkokin raya tattalin arziki, cinikayya da fasahohin kasar Sin, a wani mataki na nuna tsantsar danniya dake faruwa a duniyar yau.

Wang, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin tsakiyar JKS, ya yi tsokacin ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai na hadin gwiwa tare da mataimakin firaminista, kuma ministan harkokin wajen kasar Pakistan Mohammad Ishaq Dar a birnin Beijing.  (Saminu Alhassan)