logo

HAUSA

An Wallafa Littafin Bayanan Xi Game Da Zamanantarwa Irin Ta Sin Da Harshen Rasha

2024-05-15 20:56:56 CMG Hausa

Babbar madaba’ar tattara bayanai da fassara ta kasar Sin, ta wallafa littafin bayanai, da makaloli da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, game da zamanantarwa irin ta kasar Sin da harshen Rasha.

Littafin wanda cibiyar nazarin tarihi, da adabi ta kwamitin tsakiyar JKS ta tattara bayanan dake ciki, yana dauke da jerin muhimman batutuwa da shugaba Xi ya yi tsokaci a kansu, tsakanin watan Nuwamban shekarar 2012 zuwa Oktoban shekarar 2023, game da zamanantarwa irin ta kasar Sin.

Littafin bugun harshen Rasha, da wadanda suka gaba ce shi na harsunan Turanci da Faransanci, za su taimakawa masu karatu na kasashen waje, wajen zurfafa fahimtar tsarin dokoki, da abubuwan bukata na zahiri, domin cimma nasarar zamanantarwa irin ta kasar Sin.

Kaza lika hakan na da matukar muhimmanci wajen kyautata fahimtar sassan kasa da kasa, don gane da bukatar hada gwiwa wajen cimma burin zamanantarwa.  (Saminu Alhassan)