logo

HAUSA

Sin ta amince da a yanke hukunci mai tsanani ga masu aikata muggan laifuka don kiyaye zaman lafiya da tsaro

2024-05-15 13:47:39 CMG Hausa

 

Mataimakin wakilin dindindin na kasar Sin dake MDD Dai Bing ya bayyana cewa, Sin ta amince da yankewa wadanda suka aikata muggan laifuffuka  hukunci mai tsanani, ta yadda za a kare zaman lafiya da tsaron duniya. Dai Bing ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da kwamitin sulhu na MDD ya gudanar a jiya, kan batutuwan da suka shafi kasar Libya, wadanda kotun kasa da kasa mai binciken manyan laifuffuka ta gabatar.

Dai Bing ya ce, dole ne kotun ta gudanar da aikinsa bisa doka da oda a gaban rikici da kalubalolin dake jan hankalin duk fadin al’ummar duniya, yana mai cewa, ya kamata a aiwatar da dokar kasa da kasa bisa ka’idar adalci da kauracewar nuna ma’auni biyu da nuna bambanci, ta yadda za a kiyaye daidaito da adalci a duniya.

Ban da wannan kuma, Dai Bing ya ce, tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Libya shi ne abin da aka sa gaba wajen tabbatar da adalcin shari’a. Ya ce Sin na fatan kotun za ta nace ga ka’idar ’yancin kai da gaskiya da adalci, da kuma hadin gwiwa da mahukuntan Libya. Kazalika, kamata ya yi al’ummar duniya su mutunta ikon mulki da cikakken yankin kasar, kuma su yi goyi bayan bangarori daban-daban masu ruwa da tsaki wajen sulhuntawa da yin shawarwari tsakaninsu ta yadda za a ingiza mika ikon mulki a siyasance da kauracewa dora mata matakai na dole daga kasashen waje. Ban da wannan kuma, kotun kasa da kasa mai binciken manyan laifufuka ta gudanar da aikinsa bisa ka’idar gaggauta hadin kan bangarori daban-daban da gudun kara rarrabuwar kai a tsakaninsu. (Amina Xu)