logo

HAUSA

Matakin Amurka na kara buga harajin kwastam kan hajojin Sin babban kurkure ne

2024-05-15 20:15:52 CMG Hausa

Game da matakin kasar Amurka na kara buga harajin kwastam kan motoci masu amfani da wutar lantarki, da matattarar bayanai na laturoni ko “microchip” da Sin ta kera, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, hakan babban kuskure ne, kuma Sin za ta dauki matakai don kare hakkinta.

A daya bangaren kuma, yau Laraba 15 ga wata, ake cika shekaru 76 da fara kaddamar da hare-hare kan Falasdinawa. Game da hakan, Wang Wenbin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta ci gaba da yin kokari tare da sassan kasa da kasa, wajen sa kaimi ga daidaita batun Falasdinu cikin adalci a dukkan fannoni, da kawo karshen tashin hankali, da samun zaman lafiya a tsakanin Falasdinu da Isra’ila, da kuma a tsakanin kabilar Larabawa da ta Yahudawa.

Haka zalika kuma, kakakin ya sanar a yau cewa, bisa gayyatar da ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi masa, ministan harkokin waje, da hadin gwiwa a gabashin Afirka na kasar Tanzania, January Yusuf Makamba, zai kawo ziyara kasar Sin, daga gobe Alhamis zuwa 20 ga watan nan. (Zainab Zhang)