logo

HAUSA

Wang Yi ya taya takwaransa na Solomon murnar kama aiki

2024-05-15 14:01:40 CMG Hausa

Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya taya takwaransa na kasar Solomon Peter Agovaka, murnar kama mukamin ministan harkokin waje da cinikayya da kasashen waje.

Wang Yi ya bayyana cewa, Sin na dora babban muhimmanci kan huldar kasashen biyu, yana mai fatan kara zurfafa mu’ammalar kasashen biyu da gaggauta hadin kansu cikin harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a ingiza bunkasuwar huldarsu zuwa wani sabon matsayi. (Amina Xu)