logo

HAUSA

Shugaban Nijar ya bada umurni na a biya kudaden karatu ga daliban Nijar dake karatu a kasashen waje

2024-05-15 10:49:06 CMG Hausa

A yayin taron ministoci na ranar jiya Talata 14 ga watan Mayun shekarar 2024, shugaban kasar Nijar, janar Abdourahhamane Tiani, ya ba da umurni domin biyan kudin karatu ba tare da bata lokaci ba ga ’yan Nijar dake ci gaba da karatu a kasashen waje.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Shi dai wannan mataki zai taimakawa wajen warware matsalar kudi da wadannan dalibai ’yan Nijar suke fuskanta na matsalolin biyan kudin karatunsu a kasashen waje.

Haka kuma, ta wani bangare, a yayin wannan zaman taron ministoci da ya gudana a fadar shugaban kasa dake birnin Yamai, an yi wata sanarwa da ta shafi bada kwangilar odar kayayyakin abinci ga jami’o’in dake yankunan Nijar guda 8.

Wannan mataki zai taimaka wajen tabbatar da samar da kayayyakin abinci a kai kai ga dalibai da ke karatu a cikin jami’o’i dake cikin kasar Nijar, domin samun zarafin tabbatar da tsaron abinci da kuma kyautatuwar jin dadin dalibai.

Duk dai a cewar wannan sanarwa, ba a bada wani karin  bayani ba a karshen zaman taron ministocin da aka karanta ta gidan rediyo da talabijin na kasa RTN, game sharudan da matakai na wannan kwangila ta samar da abinci ga wadannan jami’o’i.

Sai dai wadannan matakai biyu da zaman taron ministocin ya dauka, ya bayar da gamsuwar shugabannin kungiyoyin ’yan makaranta da dalibai ganin cewa, hakan zai kara inganta rayuwar karatu na daliban Nijar dake cikin gida da waje.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.