logo

HAUSA

Ranar kasa da kasa ta jami’an jinya ko “Nurses” ta 2024

2024-05-15 08:39:39 CMG Hausa

A ranar 12 ga watan Mayun ko wace shekara ne ake gudanar da bikin ranar jami’an ba da jinya ko “Nurses” ta kasa da kasa.

Ana kuma gudanar da bikin ne a ranar da ta yi daidai da ranar haihuwar Florence Nightingale, wata jami’ar kiwon lafiya ‘yan asalin kasar Ingila, wadda tarihi ya nuna ta bayar da babbar gudummawa ga ci gaban aikin kula da marasa lafiya ta hanyar zamanantar da aiki. 

A haifi Nightingale ne a ranar 12 ga watan Mayun shekarar 1820, ta kuma rasu a ranar 13 ga watan Agustan 1910. Jami’ar kwararriya ce a fannin kididdiga, inda ta rika amfani da ilimin ta wajen samar da alkaluma dake taimakawa wajen kyautata tsarin kiwon lafiya, da rage mace macen jama’a ta hanyar aiwatar da matakan kandagarki. Don haka ne ma ake gudanar da wannan muhimmin biki na ranar jami’an jinya na kasa da kasa, a duk ranar bikin tunawa da haihuwar ta. 

A bana taken bikin ranar shi ne “Makomarmu. Moriyar tattalin arziki daga kulawa”.

A nan kasar Sin da ma sauran sassan duniya, wannan biki ya shahara, inda ake amfani da shi wajen kara wayar da kan jama’a fa’idar aikin jinya, kalubaloli da kuma ci gaban da aka sa gaba a fannin. Kaza lika, dama ce ta godewa wadannan jami’ai bisa kokarin su na tallafawa fannin kiwon lafiyar al’umma.

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, da hukumar jami’an jinya ta kasa da kasa, burin bikin na bana shi ne kyautata tunanin al’umma game da aikin jami’an jinya, da nufin fahintar da kowa muhimmancin zuba jari a fannin, da ganar da jama’a irin ribar tattalin arziki da zamantakewa da hakan zai haifar.

Baya ga aikin jinya, jami’an jinya suna wayar da kan marasa lafiya, da taimaka musu wajen fahimtar irin cutar dake damun su, da hanyoyin kula da kai har samun lafiya. Kaza lika su kan zama a tsakanin sauran jami’an kiwon lafiya da marasa lafiya a aikin magance cuta.

Kadan daga kalubalen da suke fuskanta sun hada da dora mudu aiki fiye da kima, wanda a wasu lokuta kan shafi tasirin aikin su. Sai kuma karancin kudaden albashi da alawus a wasu sassan duniya. (Sanusi Chen, Faeza Mustapha, Saminu Alhassan)