logo

HAUSA

Fadar White House Ta Sanar Da Sabbin Haraji Kan Motoci Masu Amfani Da Lantarki Na Kasar Sin

2024-05-14 19:56:02 CMG Hausa

A yau Talata, fadar White House ta kasar Amurka ta sanar da kakaba sabbin haraji kan motoci masu amfani da lantarki da batura masu aiki da hasken rana da sauran kayayyaki masu amfani da makamashi mai tsafta na kasar Sin dake shiga kasar, a wani yunkuri na kariyar cinikayya da aka yi amana zai kasance hadari ga burin Amurka na karfafa takara da rage fitar da hayakin Carbon.

Bisa shirin, haraji kan motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin zai karu daga kaso 25, zuwa kaso 100. Haka kuma, akwai wani karin kaso 2.5 na haraji kan dukkan ababen hawa da suka shiga kasuwar Amurka, inda jimilar haraji kan motoci masu amfani da lantarki na kasar Sin ta kai kaso 102.5.

Akwai yiwuwar sabon harajin da aka kara wani mataki na gwamnatin Biden na nuna matsi kan kasar Sin yayin da yakin neman zaben shugabancin kasar ya kara zafi. (Fa’iza Mustapha)