logo

HAUSA

Bikin baje kolin littattafai na kasa da kasa na Rabat

2024-05-14 10:29:03 CMG Hausa


Bikin baje kolin littattafai na kasa da kasa ke nan da ke gudana a birnin Rabat, babban birnin kasar Morroco, wanda ya kasance daya daga cikin bukukuwan baje kolin littattafai mafiya muhimmanci a nahiyar Afirka.

An dai kaddamar da bikin na bana ne a ranar 9 ga wata, kuma za a kammala shi a ranar 19 ga wata, kuma madaba’u da hukumomin al’adu sama da 700 sun halarci bikin daga kasashe da shiyyoyi 50.