logo

HAUSA

Shin Batun Kare Hakkin Bil Adama Makami Ne Kawai Na Dakile Ci Gaban Wasu Kasashe?

2024-05-14 18:52:07 CMG Hausa

Rikici tsakanin Isra’ila da Palasdinu ba sabon abu ba ne ga al’ummar kasa da kasa, amma kuma abu ne na tayar da hankali ganin yadda ake ta gadon rikicin daga zuri’a zuwa zuri’a tamkar wata al’adar gargajiya. Rikici da mace-mace batu ne da bai kamata duniya ta lamunta ba, haka kuma batu ne dake bukatar a lalubo bakin zaren warware shi tun daga tushe.

A ranar Lahadi, ofishin manyan jami’an MDD mai kula da hakkokin bil adama ya ce yanayin keta hakkin bil adama a Zirin Gaza na kara tsananta, yana mai cewa matakin Isra’ila sun sabawa dokar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa. Sai dai maimakon a ji kasashen duniya dake ganin kansu a matsayin manya kuma masu fada a ji suna daga murya game da hakan, shiru ka ake ji, sai ma kokarin da suke yi ta kowacce hanya na karawa mai cin zali karfi wajen ci gaba da aikata mummunan aikin da galibin kasashen duniya ke tir da shi. Yadda ake yayata batun kare hakkin bil adama a baki, ya bambanta da aiwatar da shi a aikace. Mun ga yadda ake matsawa kasa kamar Sin a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya a yankunanta, inda ake ta kakkaba takunkumai da bata mata suna bisa hujjar hakkin bil adama, amma aka gaza daukar matakin da ya dace kan wadanda kowa ya yi amana cewa, suna keta wannan hakki. Shin kare hakkin bil da ake yayatawa makami ne kawai na dakile kasashen dake samun ci gaba da kokarin tabbatar da zaman lafiya, maimakon kare ainihin wadanda ke bukatar kariya?

A jiya Litinin, kasar Sin ta yi kira da kasashe masu ruwa da tsaki kada su kawo cikas ga batun kasancewar Palasdinu mamba a MDD, kuma kada su ci gaba da adawa da burin kasa da kasa, ganin yadda wadannan kasashe suke hawan kujerar naki kan wannan batu. Ba sau daya ba, kasashen duniya sun bayyana burinsu na ganin an samar da zaman lafiya da tabbatar da halaltattun hakkokin Palasdinawa, amma kuma wasu kasashe na yi wa wannan buri kafar ungulu. Kasar Sin na daya daga cikin kasashen da suka dauki nauyin gabatar da kudurin kasancewar Palasdinu cikakkiyar mamba a MDD da kuma wadanda suka kada kuri’ar amincewa da shi da sauran kudurorin da suka shafi kare hakkokin Palasdinawa da tabbatar da zaman lafiya a yankin, kamar yadda ya kamata kowace kasa dake kaunar zaman lafiya ta yi.  Sai dai da alama wasu kasashe ba sa burin ganin kawo karshen wannan rikici da ma wanzuwar zaman lafiya a duniya. Kana kalaman da su kan furta na rajin kare hakkin bil adama, ya bambanta da abun da suke aiwatarwa a zahiri. Rikicin Palasdinu da Isra’ila ya kara tabbatarwa duniya wannan da kuma irin fuskoki biyu da ake nunawa a al’amuran da suka shafi kare fararen hula masu rauni. (Fa’iza Mustapha)