logo

HAUSA

Liu Wei: Ina koyar da wasan Kungfu a Afirka

2024-05-14 15:28:23 CMG Hausa

A cikin shekaru 50 da suka gabata, tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen Sin da Saliyo, dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu ya kara karfi, kuma hadin gwiwarsu a fannoni daban daban ya samu sakamako mai kyau. Kwalejin Confucius ta jami’ar Saliyo, wadda aka kafa a shekarar 2012, daya ce daga cikin sakamakon hadin gwiwar. A matsayin kwalejin Confucius ta farko a yammacin Afirka, kwalejin Confucius dake jami’ar Saliyo na taka muhimmiyar rawa wajen bunkasa harshen Sinanci, da tallata al’adun kasar Sin ga kasashen waje, da sa kaimi ga yin mu’amalar al’adu tsakanin kasahen Sin da Saliyo, da kuma ba da gudummawa ga karfafa dadadden zumuncin dake tsakanin kasashen biyu.

A cikin shirinmu na yau, bari mu yi tattaki zuwa kwalejin Confucius ta jami’ar Saliyo, inda akwai wani malami Basine, dake koyar da wasan Wushu ko kuma wasan Kungfu mai suna Liu Wei, mu ga yadda yake kokarin tallata fasahohin wasan Kungfu na kasar Sin a nahiyar Afirka.