logo

HAUSA

Hukumar kwastam a tarayyar Najeriya ta kulla yarjejeniyar kasuwanci da takwarar ta kasar China

2024-05-14 10:01:48 CMG Hausa

A farkon makon jiya ne shugaban hukumar kwastam a tarayyar Najeriya Mr Adewale Adeniyi ya jagoranci wata tawagar jami’an hukumar zuwa birnin Shenzhen na kasar Sin inda suka kalla wata yarjejeniyar kasuwanci da hukumar kwastam ta kasar Sin.

Ita dai wannan yarjejeniya kamar yadda hukumar ta bayyana cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi 12 ga wata, za ta kara karfafa harkokin tattalin arzikin kasashen biyu, ta hanya saukaka sha’anin shiga da fitar da kayayyaki ga kanana da matsakaitan masu masana’antu.

Wakilin sashen Hausa na CMG a tarayyar Najeriya Garba Abdullahi Bagwai ya tambayi jami’in yada labaran hukumar kwastam ta Najeriya Malam Abdullahi Mai-wada ko akwai wasu karin fa’idoji game da wannan yarjejeniya? 

“Fa’idar shi ne idan ka lura kayayyakin da ake shigowa da su daga China zuwa Najeriya da wanda ake fitarwa da su daga Najeriya zuwa China za ka ga wannan al’amari ne mai yawa, kuma ya kamata a zauna tare a duba a ina za a taimaki juna domin a habaka kasuwancin nan, sannan kuma a tabbatar da ganin ana yin abun da ya kamata a cikin al’amuran hukumar kwastam ta kasa, bayan nan sun baiwa juna tabbacin cewa za a yi abun da ya kamata, sannan kuma za a dabbaka abubuwan da suke cikin kundi na shi wannan yarjejeniya da aka sanyawa hannu. Sannan kuma abun da ya faru a cikin wannan tattaunawa shi ne bangaren kara samun horar da ma’aikata domin su samu gogewa, hukumar kwastam ta kasar China ta nuna cewa, kofarta a bude take domin a taimakawa juna ta hanyar tabbatar da ganin an gyara al’amura da suka shafi jami’an hukumomin kwastam na kasashen biyu, sai kuma wani bangare na ake kira E-Commerce wato tsarin kasuwancin amfani da kafar Intanet, wato dai wata sabuwar harka ce ta kasuwanci wadda kwastam yanzu a duniya tana kallon wannan al’amari domin ta ga cewa harajinta bai sha wahala ba, sannan kuma a tabbatar da cewa kasuwanci ta E-commerce an bunkasa shi.” (Garba Abdullahi Bagwai)