logo

HAUSA

Kasar Sin za ta zuba Yuan biliyan 100 domin kyautata aikin samar da ruwa a yankunan karkara a bana

2024-05-14 15:58:36 CMG Hausa

Ma’aikatar kula da albarkatun ruwa ta kasar Sin ta tsara shirin zuba kudi da yawansa ya kai Yuan biliyan 100, kwatankwacin dala biliyan 14.1, don kyautata ayyukan samar da ruwa a yankunan karkara, da kara samar da ruwan pampo ga kaso 92 bisa dari na iyalai da kamfanoni dake yankunan karkarar kasar a shekara ta 2024.