logo

HAUSA

Yunkurin Taiwan Na Halartar Babban Taron WHO Bai Yi Nasara Ba Har Sau 8

2024-05-14 21:28:13 CMG Hausa

An kammala rajistar halartar babban taron hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa WHO karo na 77 a ranar 13 ga wata. Kuma an ki amincewa yankin Taiwan na kasar Sin ya halarci taron, lamarin da bai wuce zaton mutane ba. Yunkurin mahukuntan jam’iyyar Democratic Progressive Party wato DPP na halartar taron bai yi nasara ba har sau 8. Wannan ya nuna cewa, kasa da kasa sun cimma matsaya daya kan ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”. Yadda kasar Amurka ta goyi bayan yunkurin mahukuntan jam’iyyar DPP, da neman goyon baya ta hanyoyi daban daban da mahukuntan jam’iyyar DPP su ka yi, ya yi kama da wasan yara da ba ya jan hankali.

Yankin Taiwan bai samu iznin gwamnatin tsakiyar kasar Sin na halartar babban taron WHO ba. Babu kujerarsa a babban taron. Bisa muhimman ka’idojin da aka tanada cikin kudurin babban taron MDD mai lamba 2758 da kudurin babban taron WHO mai lamba 25.1, gwamnatin jamhuriyar jama’ar kasar Sin, ita ce halaltacciyar gwamnatin da ke wakiltar Sin daya tak a duniya, wadda ke da cikakken ikon mulkin kasa cikin tsarin MDD. A matsayinsa na wani lardin kasar Sin, an bai wa yankin Taiwan damar tattauna batutuwa masu ruwa da tsaki a babban taron WHO, bisa ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”.

Haka kuma, dalilin da ya sa Amurka ta dauki shekaru da dama tana mara wa Taiwan baya wajen halartar babban taron WHO, shi ne domin wasu ‘yan siyasar Amurka suna son yin amfani da Taiwan don daukar ra’ayin rikau kan kasar Sin a shekarar bana, inda za a gudanar da babban zaben shugaban Amurka. Ban da haka kuma, Amurka tana son taimakawa Taiwan halartar babban taron WHO don kalubalantar ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya”, ta yadda za a juya wannan ka’idar don ta da hargitsi. (Tasallah Yuan)