logo

HAUSA

Sojojin Isra’ila suna kara matsa kaimin kaddamar da hare-hare a Gaza

2024-05-14 11:19:33 CMG Hausa

Rundunar Sojojin Isra’ila ta ce dakarunta na kara matsa kaimin kaddamar da hare-hare daga arewaci da kudancin zirin Gaza, inda suke luguden wuta kan wasu sassa 120 dake birnin Rafah, da wasu yankunan Jabaliya da Zeitoun dake birnin Gaza.

Cikin wata sanarwa, rundunar ta ce dakarunta na runduna ta 162 masu kaddamar da hare-hare da tankokin yaki da makaman roka, na ci gaba da harba makamai kan mayakan Hamas a gabashin Rafah, da sashen kan iyakar Gaza. Kaza lika yayin dauki ba dadi na gaba da gaba, sojin Isara’ila sun harbe mayakan Hamas da dama.

Sanarwar ta kara da cewa, sojojin Isra’ila suna gudanar da takaitattun matakan soji, da nufin kawar da ababen da mayakan Hamas ke amfani da su a Rafah.

A daya bangaren kuma, MDD ta bayyana cewa, sama da Falasdinawa 300,000 sun tsere daga Rafah tun a karshen mako, yayin da sojojin Isra’ila ke kara kusantar birnin.  (Saminu Alhassan)