logo

HAUSA

Yadda sha’anin noman abarba na taimakawa kyautata zaman rayuwar mazauna wasu kauyuka a kasar Sin

2024-05-14 14:56:21 CMG Hausa

DAGA MINA

Kwanan baya, na ziyarci kauyen Yugonglou na gundumar Xuwen dake birnin Zhanjiang na lardin Guangdong, wurin da ya shahara da noman abarba a kasar Sin. Yayin da na shiga gonakin abarba marasa iyaka, na gano dalilin da ya sa ake yiwa gonakin take da “Tekun abarba”. Mazauna kauyen dake kokarin girbin abarba sun gaya min cewa, dukkanin mazauna kauyen suna ayyuka masu alaka da abarba, don haka ana iya cewa, a kashin kan ta abarba na kawo arziki ga wannan kauye.

Alkaluman da aka samar sun shaida cewa, a shekarar 2023, fadin gonakin da aka shuka abarba a gundumar Xuwen ya kai fiye da hekta dubu 22, kuma yawan abarba da aka samar ya zarce ton dubu 788, yayin da kudin da aikin ya samar ya kai sama da dalar Amurka miliyan 751. Inda ya taimaka wajen samar da guraben aikin yi dubu 146. Ana jigilar abarba da aka girba daga gonaki zuwa kamfanonin sarrafa ta iri daban-daban, daga baya suna shiga kasuwannin cikin gida da na waje.

Amma, a shekarun baya can, mazauna gundumar Xuwen masu shuka abarba, suna takaicin rashin sayar da su, har sun rube a gonaki. Da ganin hakan, gundumar Xuwen ta gaggauta raya kanta bisa shirin gwamnatin lardin Guangdong na raya ingantattun birane da gundumomi da kauyuka, inda ba ma kawai ta kafa cibiyar samar da alkaluma dake ba da taimako ga manoma wajen zabar nau’o’in abarba da tabbatar da farashinta da sauran bangarori ba, har ma da gaggauta raya sha’anin yawon shakatawa dake da alaka da al’adun abarba.

Ta haka, na shiga otel din da aka gyara bisa gidajen mazauna kauyen,  inda na ga gonakin abarba marasa iyaka, tare da jin kamshin abarba. Ba shakka yadda ake raya sha’anin yawon shakatawa mai alaka da al’adun abarba za ta kara kudin shigar mazauna kauyen.

An ce, ko wadanne abarba uku da aka samar a nan kasar Sin, daya daga cikinsu asalin Xuwen ce. Na debi wani na dandana, ruwan abarba mai zaki ya fito nan da nan, kamshi na cike da baki na, abin da ya alamanta zaman rayuwa mai zaki ta jama’ar wannan kauye. (Mai zana da rubuta: MINA)