Bangaren samar da motoci na kasar Sin ya samu ci gaba a rubu’in farko na bana
2024-05-13 11:19:03 CMG Hausa
Sabbin alkaluma daga kungiyar masu samar da motoci ta kasar Sin sun nuna cewa, a rubu’in farko na bana, bangaren ya samu ci gaba mai inganci, inda darajar hajojin da bangaren ya samar ta karu da kashi 9.7% bisa na makamancin lokacin a bara, wanda kuma ya wuce kashi 3% na dukkan harkokin samar da hajoji.
Haka kuma, yawan kudin shiga da bangaren ya samu ya zarce dala biliyan 316, wanda ya karu da kashi 6.2% bisa na makamancin lokacin a bara.
Har ila yau, alkaluman na nuna cewa, yawan ribar da kamfanonin bangaren suka samu ya karu da kashi 32% bisa na makamancin lokaci a bara, adadin da ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 14. (Amina Xu)