Ministan tsaron Najeriya ya bukaci sojojin kasar da kada su nuna gajiyawa har sai tsaro ya tabbata a kowanne sashe na kasar
2024-05-13 09:49:27 CMG Hausa
Ministan tsaron Najeriya Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya bukaci sojojin kasar da kada su nuna gajiyawa har sai sun tabbatar da samar da dauwamammen zaman lafiya da tsaro a kowanne sashe na kasar.
Ministan ya bukaci hakan ne a karshen makon jiya lokacin da ya kai ziyarar aiki hedikwatar rundunar sojin musamman ta 8 dake Sokoto. Ya ce babu wani jam’in tsaro a Najeriya da zai sami sukuni har sai Najeriya ta shiga jerin kasashen masu cikakken zaman lafiya.
Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.
Ministan tsaron na Najeriya ya bayyana gamsuwarsa bisa irin kokarin da dakarun musamman din da aka jibge a Sokoto ke yi wajen dakile duk wasu ayyukan ’yan ta’adda ba kawai a jihohin dake shiyyar arewa maso yamma ba har ma da sauran yankuna makwafta.
Alhaji Mohammad Badaru Abubakar ya shaidawa dakarun cewa, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yana da masaniyar kalubalen da suke ciki wanda kuma ba da jimawa ba za a kawo karshensu.
Ministan wanda ya alakanta nasarorin da aka samu cimmawa wajen yaki da ’yan ta’adda a kasa baki daya bisa irin goyon bayan da shugaban kasa ke baiwa sojoji da kuma sauran jami’a tsaro.
“Muna da zakwakuran dakaru wadanda suke aiki tare da juna, kama daga babban hafsan tsaro zuwa sauran hafsoshin soji da kuma sauran hukumomin tsaro, domin kamar yadda alamu suka nuna an jima ba samun hadin kai ta fuskar aiki tare ba a tsakanin jami’an tsaron kasar nan kamar wannan lokaci.”(Garba Abdullahi Bagwai)